KWATANCIN BORIN HAUSAWA DA NA GBAGYI
By
Author
Presented To
Department of Arts
Wannan bincike ya kwatanta borin Hausa da na Gbagyi (Gwari) domin nuna
kamanci da bambanci da ke tsakaninsu. Samuwar Iskoki dai wani imani ne
da kowace al’adar al’ummar duniya ta yi imani da shi. Imanin mutanen
duniya game da Iskoki abu ]aya ne ta fuskar kasancewarsu ~oyayyu,
buwayayyu, masu ban tsoro, masu karkatar da mutane, kuma masu }arfi a
kan mutane. Shi kuma bori a matsayin bautar Iska da]a]]iyar al’ada ce,
da ke cikin hanyoyin addinin gargajiya na Hausa da kuma Gbagyi. Don
haka, ha]uwa da zamantakewa da Hausawa suka yi da Gbagyi ya haddasa
sauye-sauye na yanayin aiwatar da borin Gbagyi ta fuskokin sunayen
Iskoki ko Aljannu da halayen ‘yan bori da tufafin ‘yan bori da kayan
ki]an ‘yan bori da girka da kuma amfanin ‘yan bori ga jama’a. Wannan
bincike ya fito da wa]annan sauye-sauye a fili domin a fahimci kamanci
da kuma bambancin borin al’ummun guda biyu. Daga cikin batutuwan da aka
tattauna akwai tarihin Hausawa da Gbagyi, da borin Gbagyi na asali kafin
su ha]u da Hausawa. A farkon wannan bincike, an kawo borin Hausawa,
sannan an nuna dangantakar Hausawa da Gbagyi ta yadda suka ha]u har
borinsu ya haddasa sauyi a kan na juna musamman a manyan garuruwan
Gbagyi da aka yi bayanin ha]uwarsu kamar: Kuta da Minna da Suleja duk na
jihar Neja da kuma Birnin Gwari ta jihar Kaduna. A }arshe, binciken ya
gano matsanancin tasirin da borin Hausawa ya yi a kan na Gbagyi ta yadda
a yau, kusan dukkan ‘yan borin Gbagyi, suna aiwatar da bori ne ta salon
yadda suka ga ‘yan borin Hausawa na aiwatarwa.
PLEASE NOTE:
That this Material is a Complete Project, Well Written and Contains 1 to 5 Chapters.
Click the download Button Below to Download the complete work. OR Call/WhatsApp Admin on: 09019904113 for Inquiry. Thank You